Yanayi na kawo cikas ga ceton Korea

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rashin kyan yanayi na kawo cikas ga ceton Korea ta kudu

Wani babban jami'in kula da tekun Korea ta Kudu ya ce masu ninkaya sun samu damar isa can kasan jirgin ruwannan da ya nutse a ranar larabar da ta gabata, sun kuma samu nasarar tabo wasu abubuwa da ake kyautata zaton gawar mutane ce.

Sai dai babban jami'in Choi Sang-Hwan ya ce masu ninkayar ba sa iya ganin abubuwan da ke kasan ruwan yadda ya kamata akan ainihin abinda suka gani.

Jami'in ya kara da cewa masu ninkaya biyu sun shiga cikin ruwan tare da bude ma'ajiyar kayayyaki da ke jirgin, sai dai ba su iya shiga ciki sosai ba saboda tarkacen kaya dan haka basu gano ko mutun guda da yake da rai ba.

An dai cafke matukin jirgin da wasu kananan ma'aikatan jirgin su biyu.

Akalla mutane dari biyu da sittin da tara wadanda yawancinsu yara 'yan makaranta ne dai ba a gano ba, ya yin da aka tabbatar da gano gawawwakin mutane ashirin da tara.

Karin bayani