Mu muka kai harin Nyanya - Shekau

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar Boko Haram ta ce itace ta kai hare-haren bama-baman da su ka halaka kimanin mutane 75 a tashar Nyanya dake kusa da Abuja.

A cikin wani sakon bidiyo da aka aika wa kafofin yada labarai, shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce su ne keda alhakin kai harin.

Shekau ya yi ikirarin cewa 'yan Boko Haram din da su ka kai harin na zaune ne cikin Abuja.

A sakon na bidiyo mai tsawo minti 28, wanda 'yan kungiyar su ka bayar ranar Asabar, shugaban nasu ya yi magana da harsunan Larabci da kuma Hausa.

Shekau dai na sanye ne da kayan soji, ga kuma bindiga akan kafarsa, lokacin da ya ke kalaman nasa.

Hare-haren bama-baman, wadanda aka kai a Nyanya a ranar Litinin, su ne mafi muni da aka kai wa birnin Tarayyar Najeriyar.

Karin bayani