PDP da APC na zargin juna kan hare-hare

Image caption Nyako ya zargi Gwamnatin TArayya da halin ko in kula kan rashin tsaro

A Najeriya duk da cewa Kungiyar Boko Haram na daukar alhakin kai harin Bam a Abuja da Kuma wadanda ake ci gaba da kai wa a shiyyar arewa maso Gabashin kasar, Jam'iyyar PDP Mai mulki da Kuma babbar jam'iyyar adawa ta APC na ci gaba da zargin juna da hannu ko masaniya game da hare- haren.

Jamiyyar PDP ce ta fara zargin APC da alaka da hare-haren ta'addancin da aka kai Abuja da kuma kauyuka a Borno tana mayar da martani ne da rashin halartar gwamnonin Jamiyyar APC suka yi.

Su ma dai gwamnonin Jamiyyar APC na zargin gwamnatin Tarayya da shirya kai hare-haren saboda halin ko in kula da suka ce Shugaba Jonathan ke nunawa; suna cewa bayan kai harin da aka kai Nyenya a Abuja da kwana daya ya tafi Kano don halartar bikin siyasa.

Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako a wata doguwar wasika da ya fitar ranar Juma'a inda yake zargin gwamnatin Tarayya da tsara hare-haren ya kuma yiwa magoya bayan Jamiyyar APC jawabi kan zargin da yake yi kan hare-haren.

Nyako ya ce, "da dama Alla-Allah ake ayi fada kan kabilanci ko addini, ko a kan batun a ina aka haife mu to wannan ba ya cikin addininmu".

Karin bayani