An sako 'yan jaridar Fransa a Syria

Hakkin mallakar hoto n
Image caption 'Yan jaridar Faransar nan da aka sako a Syria sun nufi gida

'Yan jaridar nan su hudu 'yan asalin Faransa da aka sako su daga Syria wadanda aka kama kusan shekara guda suna kan hanyar su ta komawa kasarsu.

Ana sa ran za su isa Pari da safiyar nan a cikin wani jirgin Sojin Faransa da ya dauke su a kasar Turkiyya.

Shugaba Francois Hollande da iyalansu ne dai za su tare su a filin jirgin sama.

Tun da fari dan uwan Nicolas Pron-Ay-Nan daya daga cikin 'yan jaridar ya shaidawa BBC cewa ba bu wata musgunawa ta zahiri da aka yi musu.

An dai sace 'yan jaridar ne a bara da ake zargin wata kungiya mai alaka da al-qaeda da sace su; an kuma tsince su a iyakar Syria da Turkiyya a jiya Asabar.

Karin bayani