Mabiya addinin Kirista na bukin Easter

Shugaab Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kiristoci a sassa dabn-daban na duniya ne ke gudanar da bikin ana Easter.

Bikin Easter na daya daga cikin bukukuwa mafiya muhimmanci ga mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya da ake yi shekara-shekara, kuma yanzu haka ma suna gudanar da shagulgulan easter na bana.

Yayin da ake bikin, Rabaran Dokta Shuaibu Byel, shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN, reshen arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya bayyana manufar bikin na Easter da muhimmancin sa ga mabiya addinin kirista da kuma muhimman darussan da suke cikin lokacin da ma yadda ya kamata dukkan Kirista na kwarai ya kamata ya gudanar da shi.

Dokta Byel ya kuma yi kira ga mabiya addinin Kirista da su yi amfani da wannan lokaci wajen yiwa Najeriya addu'o'i na musamman kan matsalar tabarbarewar tsaro da ke addabar kasar.