Chibok: 'Yan mata 77 suka rage

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana zargin 'yan Boko Haram sun kai 'yan mata dajin Sambisa ne

Gwamnatin Jihar Borno da ke arewacin Nigeria ta ce a yanzu saura dalibai 'yan mata 77 suka rage daga cikin 129 da 'yan Boko Haram suka sace a makarantarsu a Chibok.

Sanarwa daga gwamnan jihar, Alhaji Kashim Shettima ta ce kawo yanzu 'yan matan sakandare na Chibok su 52 ne suka kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

A ranar Lahadi aka gano wasu karin 'yan mata su 7 wadanda suka tsere daga hannun masu garkuwa dasu wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Gwamna Shettima ya ce duk da cewar ya hau mulki ana rikicin 'yan Boko Haram, amma dai makon da aka sace dalibanne mako mafi muni gare shi tun da ya soma mulkin jihar ta Borno.

Ya kara da cewar a yanzu abun da ya rage shi ne a cigaba da addu'a don gannin cewar sauran 'yan matan sun kubuta.

Shettima ya kuma bayyana cewar akwai bukatar a cigaba da baiwa jami'an tsaro hadin kai tare da sauran 'yan banga da mafaraunta wadanda ke ci gaba da laluben wadannan 'yan matan da aka sace.

Karin bayani