Rasha ta zargi Ukraine da saba alkawari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Sergie Lavrov

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya zargi hukumomin kasar Ukraine da keta yarjejeniyar da aka cinma a Geneva a makon jiya, domin warware rikicin kasar.

A cewarsa gwamnati a birnin Kiev ba ta dauki matakin karbe makamai a hannu kungiyoyin dakarun sa kai, masu dauke da makamai ba, musamman ma 'yan kungiyar masu kaifin kishin Ukraine, ta Right Sector.

Lavrov yace "Muhimmin abu a yanzu shi ne a hana aukuwar duk wani tashin hankali, wanda kuma shi ne batu na farko a yarjejeniyar Geneva".

A lokacin hira da manema labarun, Mr Lavrov ya kuma yi Allah wadai da mummunan harin bindiga da aka kai a ranar Lahadi, a wani wurin binciken ababen hawa na masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine.

Hakan a cewarsa alama ce da ke nunawa Ukraine ba ta da niyyar tsawatawa masu tsattsauran ra'ayi.

Karin bayani