Hukuncin kisa kan mutane 5 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Kotu a Saudi Arabia ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin kisa saboda rawar da suka taka a jerin hare-haren kunar bakin wake a shekara ta 2003.

Kafafen yada labarai a Saudiyya sun ce wasu karin mutane 37 suma an yanke musu hukuncin zama a gidan kaso bisa hannu a hare-haren da aka kashe mutane a Riyadh babban birnin kasar.

Hare-haren sun janyo aka soma yaki da mayakan kungiyar Al Qaeda a Saudi Arabia.

Tashi tsayen da hukumomi a Saudiyya suka ya tilastawa wasu 'yan Al Qaeda din suka koma kasar Yemen don ci gaba da gwagwarmaya.

Amurka na kallon kungiyar Al-Qaeda a kasashen Larabawa a matsayin kungiya mafi hadari.

Karin bayani