An kashe dalibi dan Najeriya a Ghana

Taswirar Ghana
Image caption Taswirar Ghana

A Ghana 'yan sanda a birnin Cape Coast a yammacin kasar, sun ce sun kama wasu dalibai 'yan Najeriya guda biyar, bisa zargin kisan wani dan'uwansu dalibi dan Najeriyar, Chukudi Ayogu.

Dukansu dai daliban jami'ar Cape Coast din ne.

'Yan sandan dai sun ce kisan yana da nasaba da lamarin kudi da ya shiga tsakanin Chukudi Ayogu da daya cikin daliban.

An yanka dalibin ne tare kuma da daddaba masa wuka.

A Ghana akwai daruruwan dalibai 'yan Najeriya da ke karatu a jami'o'i da kwalejoji, sakamakon wasu matsalolin da ake fuskanta a Najeriyar.