Novartis da GSK sun kulla yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yarjejeniyar ta dubban daloli suka kulla

Novartis da GlaxoSmithKline, kamfanonin hada magunguna mafi girma a duniya sun kulla wata yarjejeniya ta biliyoyin daloli.

Hadin gwiwar ta shafi batun sake fasalin harkar kasuwancinsu.

Kamfanin GSK, na Birtaniya, ya sayi harkar hada allurar riga kafi na Kamfanin Norvatis a kan kudi dola biliyan 7, yayinda ya sayar da sashen hada maganinsa na ciwon daji ko cancer ga Kamfanin na Switzerland, Norvatis a kan kudi dola biliyan 16.

Kamfanonin biyu za su kuma hada gwiwar kasuwanci, ta hanyar sayar da magungunan sayi-ka-tafi da kuma kayan shafe-shafe.