Chibok: 'Yan Mata kusan 180 suka rage

Image caption 'Yan Boko Haram sun yi garkuwa da 'yan matan

Mako guda bayan da aka sace wasu dalibai 'yan mata a makarantarsu da ke Chibok a Jihar Borno, har yanzu akwai sauran 'yan mata 180 a hannun 'yan Boko Haram.

Iyaye da 'yan uwan wadanda aka sacen suna cikin damuwa inda suka bukaci 'yan Boko Haram su taimake su sako musu 'ya'yansu.

Daya daga cikin iyayen yaran ya shaidawa BBC cewar yana fatan gwamnati za ta yi sulhu da 'yan Boko Haram don 'ya'yansu su kubuta.

Shugabar makarantar, Mrs Asabe Kwambura ta bayyanawa BBC cewar adadin 'yan matan da aka sace ya zarta adadin da gwamnatin ke cewa.

Kwambura ta ce "Mun bude rijista inda iyayen da aka sace 'ya'yansu suka rubuta sunayen 'ya'yan, kuma rijitarmu ta nuna cewar 'yan mata 230 aka sace, sannan 43 sun kubuta".

A cewarta "Allah ne ya kubutar da 'yan matan, babu wani soja ko jami'in tsaro da ya kubutar da su. Basirarsu ce ta cecesu".

Kawo yanzu gwamnatin Shugaba Jonathan ba ta ce komai ba game da yinkurin ceto 'yan matan, a yayinda iyayen yaran suka ce sun shiga daji amma basu ga wani jami'in tsaro ba.

A makon da ya gabata dakarun tsaron Nigeria sun ce ana aikin hadin gwiwa tsakanin sojin sama da na kasa domin ceto 'yan matan.

Karin bayani