An gano gawawwaki sama da 100 a Korea ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gawwakin da aka gano sun zarta 100 a Korea ta kudu

A yanzu haka adadin mutanen da suka rasa rayukansu a jirgin ruwan Korea ta Kudu da ya nutse a makon da ya wuce ya kai fiye da dari.

Kusan mutane dari biyu ne dai har yanzu ba a gano ba, yawancinsu yara ne 'yan makarantar sakandare da ke kusa da Seoul babban birnin kasar.

A jiya Litinin an samu ci gaba da aikin da masu ninkaya suke yi inda sukai nasarar sake zakulo wasu gawawwakin.

Wakilin BBC a tsuburin Jindo ya ce za a fito da baki dayan jirgin daga ruwan a ranar Alhamis din nan.

Karin bayani