A kara matakan tsaro a gabashin Ukraine

Shugaban Ukraine na riko Oleksandr Turchynov
Image caption Shugaban Ukraine na riko Oleksandr Turchynov

Shugaban Ukraine na riko, Oleksandr Turchynov, ya bukaci hukumomin tsaron kasar da su sake kaddamar da abinda ya kira: matakan yaki da 'yan ta'adda a gabacin Ukraine din.

Mr Turchynov ya ce an samu gawar wasu mutane biyu da aka gallazawa da suka hada da wani dan siyasa daga jama'iyarsa.

Lamarin ya faru ne a wajen garin Sloviansk da ke karkashin ikon sojin sa kai masu goyon bayan Rasha.

Tun farko sojin sa kan sun kwace hedkwatar 'yan sanda a Kramatorsk mai makwabtaka da wurin, sannan suka sace shugaban 'yan sandan.

A ziyarar da ya kai yau a Kiev, babban birnin kasar ta Ukraine, mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce dole ne Rasha ta daina magana kawai, ta soma aiki domin kwantar da hankali a rikicin.

An shirya ziyarar ta Mr Biden ce domin nuna irin kwakkwaran goyon bayan gwamnatin Amurka ga hukumomin rikon Ukraine.