Iyaye za su yi zanga-zanga a Chibok

Image caption Wasu daga cikin 'yan matan da suka kubuta

Iyayen 'yan matan da aka sace a makarantar sakandare ta Chibok da ke jihar Borno za su gudanar da zanga-zanga domin neman a saki 'ya'yansu.

Kwanaki takwas kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata 230 a makarantar amma fiye da 50 sun kubuta a yayinda kusan 180 suke hannun 'yan kungiyar.

Iyayen yaran na zargin cewar gwamnati ta gaza a kokarinta na kubutar da 'ya'yansu, inda wadansunsu suka shiga daji neman 'ya'yan amma ba suga jami'an tsaro ba.

Haka kuma za a gudanar da wata zanga-zangar lumana a dandalin Eagle da ke Abuja domin matsawa gwamnati lamba ta tashi tsaye wajen kokarin lalubo inda aka boye 'ya'yan.

Masu zanga-zangar a Chibok da Abuja sun ce a ranar Alhamis ne za su gudanar da zanga-zangar.

Da dama na kallon gwamnatin Shugaba Jonathan a matsayin wacce ba ta bada fifiko ga tsaron 'yan kasar da dukiyarsu.

Sai dai 'yan koran shugaban na cewar gwamnati ta himmatu wajen magance matsalar Boko Haram da sauran matsalolin tsaro a kasar.

Karin bayani