An kashe babban dan sanda a Masar

Hakkin mallakar hoto Rueters
Image caption 'Yan sanda a Masar na arangama da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

Jami'an tsaron Masar sun ce an kashe wani babban dan sanda ta hanyar wani harin bom a Alkahira.

Sun ce Birgediya Janar na 'yan sanda, Ahmed Zaki ya mutu ne a wata unguwar yammacin babban birnin, bayan da wani bom ya tashi a karkashin motarsa.

A Eskandariya kuma, an harbe wani jami'i na biyu, Laftana Ahmed Saad a lokacin wani samame a kan abinda ma'aikatar cikin gida ta ce, wata maboyar 'yan gwagwarmaya ce.

Haka nan kuma an kashe wani wanda ake zargi da hannu a tada kayar baya.

'Yan gwagwarmayar Islama a Masar sun zafafa hare-harensu a kan dakarun tsaro tun hambarar da Shugaba Mohammed Morsi a cikin watan Yulin bara.

Karin bayani