Bafaranshe ya mutu a hannun Mujao

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gilberto Rodrigues Leal

'Yan fafutuka masu kishin Musulunci a kasar Mali sun ce wani Bafaranshe da suke garkuwa da shi, Gilberto Rodrigues Leal ya mutu.

Kungiyar Mujao mai alaka da al-Qaeda ta fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Bafaranshen ya mutu, saboda a cewarsu "Faransa abokiyar gaba ce", ko da yake dai babu wani tabbaci a hukumance kan mutuwar Bafaranshen mai shekaru 62.

A makon da ya wuce dakarun Faransa a Mali sun kubutar da ma'aikatan agaji 5 da aka sace a arewacin kasar tun cikin watan Fabrairun bana.

AFP ya ce an samu labarin mutuwar, Rodrigues Leal ne a wata takaitacciyar tattaunawa ta wayar tarho da mai magana da yawun kungiyar ta Mujao, Yoro Abdoul Salam.

Duk da yake, bai ba da cikakken bayani kan rana ko yanayin da Bafaranshe ya mutu ba, amma da aka tambaye shi, (Yoro Abdoul Salam) ya ce "Da Sunan Allah, Ya Mutu" sannan ya ajiye waya.

Ofishin Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce mai yiwuwa ne Mr. Rodrigues Leal ya mutu makonni da dama da suka wuce saboda azabar da ya sha a hannun masu garkuwa da shi.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce "duk abin da za ta yi don binciko gaskiyar abin da ya faru...kuma ba za ta bari wannan abu ya wuce ba tare da hukunci ba".

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce sanarwar da aka samu daga kungiyar 'yan ta'adda ta Mujao "wadda ke da hannu a sace Rodrigues Leal, ta sa mu yarda a yau cewa mai yiwuwa wanda ake garkuwar da shi ya mutu, duk da yake babu wata shaida da za ta sa mu yarda da haka".

Kasar Mali ta tsunduma cikin yamutsi shekaru biyu da suka gabata lokacin da tawayen Azbinawa da ke yankin arewacin kasar ya janyo juyin mulkin soja.

Karin bayani