Kotu ta ce a jefe wani tsoho a Kano

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda a Kano sun ce ana samun karuwar Fyade a jihar

Wata Kotun Shari'a a Jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Kotun ta samu, Ubale Sa'idu ,wanda manomi ne, da laifin yi wa wata yarinya 'yar kimanin shekaru 10 fyade.

An ce mutumin mai shekaru 63, ya sa wa yarinyar kwayar cutar HIV mai rikidewa ta zama AIDS.

A cikin wata hira da BBC, kwamishinan shari'a na jihar ta Kano, Barr Maliki Kuliya, ya tabbatar da yanke hukuncin, yana mai cewa, a karkashin doka, mutumin na da ikon daukaka kara cikin wata guda.

Matsalar fyade dai matsala ce da ake cewa tana karuwa a Kano, da ma a sauran sassa na Nijeriya.

Karin bayani