Za mu gaya wa Jonathan gaskiya - Nyako

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi wani taro da gwamnonin jihohi 36, domin tattauna matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya ce batun tsaro a Nigeria ya kai matsayin da ya zama dole su yi wa shugaba Jonathan bayani.

Gwamnonin jam'iyyar adawa ta APC sun ce a shirye suke su halarci taron na ranar Laraba, domin tattauna batun na tsaro.

A makon jiya shugaban ya yi irin wannan taron da 'yan majalisar tsaro ta kasa da wasu gwamnonin.

Sai dai gwamnonin na APC ba su halarci taron ba, inda suka ce yaudararsu aka yi cewa an dage taron.

Mai yiwuwa dai a tabo batun dokar ta-bacin da aka kafa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a taron, wanda ya kare a karshen mako.