An kashe 35 a wani kauye a Wukari

Image caption 'Yan sanda Nigeria

Rahotanni daga jihar Taraba a arewacin Nigeria na cewa mutane akalla 35 sun rasu sakamakon wani hari da aka kai a Kauyen-Yaku da ke Wukari a Jihar Taraba.

Wasu 'yan bindiga ne suka kai mummunan hari inda lamarin ya janyo jikkatar mutane da dama sannan wasu kuma kusan 15 suka bata.

Hukumomin tsaro a jihar Taraba sun tabbatar da afkuwar lamarin amma sun bayyana cewa mutane goma sha bakwai ne suka gano wadanda suka rasa rayukansu.

Shugaban matasan kabilar Jukun a karamar hukumar ta Wukari, Mista Zando Hoku, ya shaida wa BBB cewa maharan da suka aikata kashe-kashen sun dirar wa garin ne a ranar Talata da bindigogi.

Sannan kuma a cewarsa suka cinna wa illahirin gine-ginen dake kauyen wuta.

Jihar ta Taraba dai na daya daga cikin jihohin da a baya-bayan nan ke fama da kashe-kashen mutane musamman a kananan hukumomin Wukari da Ibi.

Rikicin na da nasaba da addinni da kuma kabilanci.

Karin bayani