Kasuwar wayar iPhone ta yi kyau

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wayoyin Apple sun soma kasuwa a China

Katafaren kamfanin kera wayar salula-Apple ya ce ya ci ribar $10.2 biliyan a watanni ukun farko na bana, bayan sayar da wayoyin iPhone fiye da miliyan 43.

Kamfani ya kuma bayyana shirin sayen hannayen jari na $30bn daga masu zuba jarinsa, inda kuma zai kara ribarsu ta watanni uku-uku da kaso 8 cikin 100.

Ya ce zai kara wa masu hannun jari hajarsu a karon farko cikin shekaru 9, a yunkurin dadada musu yayin da kamfanin ke fuskantar raguwar kudaden shiga.

Darajar hannayen jarin Apple ta yi sama da fiye da kaso 7 cikin 100 a kasuwar hada-hadar hannayen jari, bayan tashi daga kasuwa, yayin da masu jari ke maraba da labarin karin hannun jari daya a kan hannayen jari bakwai da suka mallaka, matakin da zai fara aikin a watan Yuni.

'Gagarumin Ciniki'

Dumbin cinikin wayoyin iPhone ya bai wa masharhanta mamaki, wadanda suka yi tsammanin faduwar cinikin kamfanin bayan hutun kirismeti.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasuwar iPad ta fadi

Cinikin wayar iPhone, wadda ita ce hajar Apple mafi karbuwa, ya taimaka wa kamfanin da fiye da rabi na kudin shigarsa, wadda ya ja-baya da kaso 14 cikin 100 a watannin uku na karshe a bara, yayin da masu sayayya ke jiran fitowar sabbin wayoyi.

Sai dai, cinikin Apple ya karu da kaso 17 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar da ta wuce.

Babban jami'in kamfanin Tim Cook a wata sanarwa ya ce "Muna matukar alfahari da sakamakon da muke gani a watanni ukun farko na wannan shekarar, musammam gagarumin cinikin wayarmu ta iPhone da kuma kudin shigar da muka samu daga aikace-aikacenmu".

Haka zailka a wani taron manema labarai don tattauna ribar kamfani, Tim Cook ya kara da cewa wannan wani muhimmin lokaci ne ga Apple.

Ya ce kamfanin ya samu kamfanoni 24 a watanni 18 na baya don inganta ayyukan bincike da bunkasa sabbin fasahohi da kayayyakin Apple.

Kamfanin na fuskantar gasa mai zafi daga takwaransa Samsung, da ke sayar da wayoyin salula na zamani mafi rahusa, da galibi ke da fasahar Android mai ba da damar shiga shafin matambayi ba ya bata.

Haka kuma, sabon babban jami'in kudi na kamfanin, Lucas Maestri ya sake bai wa masu zuba jari tabbaci a kan kwamfutar hannu ta iPad, wadda kasuwarta ta fadi da kaso 16 cikin 100, faduwa mafi girma da hajar ta taba fuskanta.

Karin bayani