Ebola ta kashe mutane 136 a Guinea

Hakkin mallakar hoto MSF
Image caption Ta hanyar gwaji ne aka gano fiye da rabin masu dauke da cutar

Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ta ce mutane 136 ne suka mutu daga cikin mutane 208 da suka kamu da cutar Ebola a kasar Guinea.

Cutar Ebola ba ta da magani, amma idan aka sha magani cikin gaggawa, jikin mara lafiya kan samar da kariya daga cutar.

Shaida

Wani wanda ya kubuta daga cutar, kuma ba a bayyana sunansa ba, ya yi wa BBC karin bayani.

Yace "Cutar na farawa da ciwon kai da gudawa, sai ciwon baya da kuma amai. "

"Likitan da na fara gani a kauyenmu ya gaya mini cewa zazzabi ne ke damu na, amma lokacin da aka kai ni wani asibiti dake Conakry na fahimci cewa na kamu da cutar Ebola ne." In ji mutumin

"Na sha jin labarin cutar, saboda haka lokacin da likita ya shaida mini ina dauke da Ebola, sai na shiga damuwa da kuma fargaba."

"Na yi tunanin mutuwa amma dai watakila lokaci ne bai yi ba, da haka dai na samu nasarar shawo kan ciwon da kuma tsoron dake damuna.

Yace,"Likitoci daga kungiyar Medecins Sans Frontiers (MSF) sun kara mini karfin gwiwa matuka ta hanyar taimakamin."

Hakkin mallakar hoto AFP

A wani lokaci can baya, na yi zaton zan mutu lokacin da wasu 'yan uwan mahaifa na biyu suka rasu na ga an fita da gawarsu.

A wannan daren ba wanda ya iya barci, munyi tsammanin ba zamu wayi gari ba.

Wasu likitoci daga MSF ne suka rufe gawawwakin tare da sanya magani a wurin. Duk wadannan al'amura sun faru a gaba na."

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba