Shugaba Jonathan da gwamnoni sun gana a kan tsaro

taswirar Najeria

A Najeriya, dazun nan ne aka kammala wani taro da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi da manyan jami'an tsrao, da gwamnoni, da kuma shugabannin addini na kasar.

Sun tattauna a kan matsalolin tsaro da dama da suka addabi kasar, musamman rikicin Boko Haram, da na Fulani..

Gwamnan jihar Neja ya yi wa ‘yan jarida karin bayani a kan batutuwan da suka tattauna a taron.

Ya ce an tattauna matsalolin tsaro da dama, wadanda suka hada da batun Boko Haram, da na Fulani da manoma a jihohin Neja da Kaduna da Zamfara.

Sun kuma yi kira ga kowa ya taimaka wajen tabbatar da tsaro – jama’a, da talakawa da kuma jami’na tsaro.