Majalisar tsaro ta tattauna kan kame 'yan matan Chibok

Image caption Shugaba Jonathan na shan suka game da tsaron Nigeria

Batun 'yan matan nan da aka sace a makarantar Sakandiren Chibok da ke jihar Borno, na daga cikin batutuwan da suka kankane tattaunawar koli da ta shafi tsaro da Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya jagoranta.

An gudanar da taron ne da gwamnonin jihohin kasar, da shugabannin fannin tsaro da kuma malaman addinai a ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya shaida wa manema labarai cewa, taron ya amince cewa babban batun da ke jan hankali a yanzu shi ne sace 'yan matan na Chibok.

A don haka taron ya amince cewa dole ne a dauki matakai cikin gaggawa don a ceton 'yan makarantar da aka sace.

Gwamnan na jihar Ekiti ya kuma ce, jami'an tsaro sun basu tabbacin cewa suna kokarin kwato 'yan matan daga hannun wadanda suka sace su.

Shi ma ministan tsaron Najeriya Aliyu Gusau ya ce taron ya tattauna a kan dukkan matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta wadanda suka hadar da hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, da sace-sacen shanu, da satar mutane da sauran miyagun laifuka.

Manyan hafsoshin tsaron kasar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda da kuma manyan jami'an tsaro duk su ma sun halarci tattaunawar.

An gayyaci Sultan na Sokoto da Shugaba kungiyar Kiristoci-CAN duk don su bada tasu gudunmuwar a taron.

Tattaunawar ta zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro musamman na ayyukan ta'addanci da ake zargin 'yan Boko Haram da aikata wa.

Karin bayani