Matakan tsaro kan iyakokin Nijar da Najeriya

Niger border security Hakkin mallakar hoto
Image caption Niger border security

Hukumomin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar sun ce sun dauki kwararan matakan tsaro a kan iyakokinta da Najeriyan don samar da zaman lafiya.

Jihar Diffa dai na kan iyakoki da jahohin Borno da Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

To, sai dai wasu 'yan kasar mazauna yankin na ganin akwai bukatar jami'an tsaron kasar su sake salon aiki, idan suna son cafke masu mugun nufi da ka iya ketaro iyaka da niyyar aikata assha.

Matsalar tsaron na daga cikin manyan kalubalen da mahukuntan Nijar ke fuskanta a kan iyakokin kasar da makwabciyarta Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram.

Hukumomin jihar Diffa Malam Yakubu Usmana Gawo ya ce suna daukar manyan matakan na tsaro a kan iyakarsu da jihohin Najeriyar da suke makwabtaka da su.