Isra'ila ba ta ji dadin daidaitawar Falasdinawa ba

Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto AP

Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya ce dole ne jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya soke 'yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar Hamas, idan dai har yana son a cigaba da tattaunawar sulhun da Amurka ke mara wa baya.

A wata hira da BBC Mista Netanyahu, ya ce Mista Abbas yana da zabi guda ne, ko dai ya yi sulhu da Isra'ila ko kuma ya kulla 'yarjejeniya da Hamas, amma ba zai iya yin duka biyu ba.

Ya ce, “Matsawar ina kan mukamin Pira ministan Isra'ila, ba zan taba tattaunawa da wata Hukumar Falasdinawa da ta kunshi Hamas ba, wadda kungiya ce ta 'yan ta'adda da suka kuduri aniyar kawar da Isra'ila.”

A jiya ne dai kungiyoyin Fatah da Hamas suka sanar cewa sun amince su kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kan kasa, shekaru bakwai bayan rikicin da suka yi kan batun iko da Zirin Gaza.

Bayan Isra’ilar, ita ma Amurka ta yi Allah wadai da sasantawar da aka samu tsakanin Hamas din da Fatah.