Saudiyya na hana yaduwar cutar numfashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana kamuwa da cutar ne ta iska, kuma ba ta nuna wa a fuska ko a jiki

Hukumomi a Saudiyya na cigaba da daukar matakan hana yaduwar cutar nan dake shafar numfashi, mai suna MERS mai saurin kisa.

Yanzu dai an gano cewa karin mutane 11 sun kamu da cutar, a garuruwan da suka hada da birnin Makkah.

Ya zuwa yanzu cutar ta hallaka mutane 81 a kasar ta Saudiyya.

Kwayar cutar na da yanayi da cututtukan HIV da cutar murar tsuntsaye, kuma tana kawo zazzabi da daukewar numfashi sai mutuwa.