Labaran BBC Hausa a BBM

Image caption BBC Hausa- Labaran duniya a duk inda kuke

Daga yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa a kan wayoyin salularku a shafin BlackBerry Messenger a Nigeria da sauran kasashen duniya.

Tsarin samar da labaran na BBC Hausa wani hadin gwiwa ne tsakanin Sashen BBC mai watsa shirye-shirye a kasashen duniya da kuma kamfanin BlackBerry.

A duk rana za a dunga samun sabbin labarai biyar daga sashin Hausa na BBC.

Domin samun labaran sai ku duba shafinmu na BBM mai lamba C00334DDD.

Kaddamar da labaran BBC Hausa a BBM wani sabon tsari ne na samarwa jama'a labarai a duk inda suke.

Editan BBC Hausa, Mansur Liman ya ce "Samar da labarai a BBM zai bada damar samun sabbin abokan hudda ta wayar salula a Nigeria."

Mataimakin Editan Labarai na BBC, Trushar Barot ya ce "An shafe watanni ana tattaunawa da BlackBerry a kan tsarin, kuma samar da labaran BBC Hausa a BBM dama ce ga 'yan Nigeria masu amfani da BBM."

Domin shiga shafi na BBM, masu amfanin da wayoyin salula na bukatar nemo kalmar BBC Hausa daga jerin shafukan da ake da su.

Ko kuma, ta shafinmu na intanat, watau BBChausa.com

Kada ku manta lambar PIN din namu ita ce C00334DDD.

Karin bayani