Jonathan ya daina gangamin siyasa - APC

Shugaban APC Bisi Akande
Image caption Jonathan ya soke ziyarar da ya shirya zuwa Oyo, a ranar da aka kai harin na Abuja

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta bukaci shugaba Goodluck Jonathan, ya dakatar da gangamin siyasar da ya shirya yi a jihar Adamawa a ranar Talata mai zuwa.

Jam'iyyar ta ce bai dace ba shugaban ya ci gaba da buki ba, kasancewar har yanzu ba a ga 'yan matan nan kusan 200 da aka sace a Chibok ba.

APC ta kara da cewa bai kamata shugaban ya maimaita abin da ta kira kuskuren da yayi a makon jiya ba, inda aka gan shi yana rawa a gangamin siyasa a Kano, kwana daya bayan harin bam ya kashe mutane sama da 70 a Abuja.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce idan aka tsayar da al'amuran gwamnati, masu tada kayar baya za su ga kamar sun yi nasara ne.