Za mu kawar da cutar zazzabin cizon sauro - WHO

Zazzabin cizon sauro Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Zazzabin cizon sauro

A wannan rana ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro, Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta yi alwashin kawar da cutar.

Taken ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauron na duniya a wannan shekjarar shine ''A dauki makamai a kuma, don a samu galaba kan cutar zazzabin cizon sauro''.

Cutar na hallaka dubun dubatar jama'a a kasashen Afirka a ko wace shekara da akasarinsu kananan yara ne.

A shekara ta 2000 ne adadin wadanda ke mutuwa sakamakon cutar zazzabin cizon sauron a yankin kudu da hamadar Afirka ya ragu da akalla rabi.

WHO din ta ce nasarar na da nasaba da hobbasan da gwamnatocin suka yi na yaki da cutar ta hanyar amfani da kudade masu dama wajen dakile ta.

Sai dai a wani rahoto da ta bayar ya nuna cewa Najeriya na sahun gaba da alkaluma mafi rinjaye na mutanen dake mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a duniya.

Rahoton ya kara da cewa hakan ya biyo bayan karancin masu amfani da gidan sauro ne da aka yi wa feshin magani.