Sabuwar cuta ta kashe mutane 5 a Saudi

Hakkin mallakar hoto Getty

Ma'aikatar kiwon lafiyar Saudiyya ta ce sabuwar cutar MERS da bata da magani ta hallaka mutane biyar a kasar.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar zuwa 92.

A kasar Masar ma an bada labarin cewa wata mata mai shekaru 28 da bata jima da dawowa daga Saudiyya ba ta kamu cutar

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin internet na ma'aikatar kiwon lafiyar Saudiyyar ta ce an samu karin mutane 14 da suka kamu da cutar.

Hakan na nufin mutane dari-ukku-da-goma-sha ukka ne suka kamu cutar tun bayan bullarta watanni 18 da suka wuce