'Syria na da sauran makamai masu guba'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugabar kwamitin da ke sa ido akan raba Syria da makamanta na guba, Sigrid Kaag tace har yanzu kasar na da kusan kashi takwas bisa dari na makaman.

Sigrid Kaag tace koda yake an cire yawancin makaman, amma dai ba a kaiga lalata su ba.

Misis Kaaag ta kuma ce Syria na cika duk alkwarunda ta dauka wajen mika makaman nata