Mun amince da takunkumi kan kasar Rasha- G7

Mayakan sa-kai masu goyon bayan Rasha a Sloviansk Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan sa-kai masu goyon bayan Rasha a Sloviansk

Shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta duniya G7 sun amince da gaggauta takunkumin da ake neman kakabawa kasar Rasha.

G7 din dai ta ce Rashar na ingiza wutar rikicin dake faruwa a Ukraine, tana mai nuna damuwarta kan yadda 'yan awaren ke goyon bayan Rasha suke kara azamar wargaza gabashin Ukraine.

A baya bayan nan dai sojin sa-kai masu goyon bayan kasar Rasha dake birnin Sloviansk gabashin kasar Ukraine sun kama wata tawagar mutane 13 na masu sa ido na kasa da kasa 'yan kasar Ukraine.

Sun dai kai ziyara ne yankin, a daya daga cikin ayyukansu mai alaka dakungiyar hadin kai da tsaro ta kasashen Turai.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta bada bayanan cewa ana tattaunawa kan yadda za a sako su.

Mai magana da yawun ofishin huddar jaadancin Amurka Jean Psaki ta ce yin garkuwa da mutanen ba abu ne da za a amince da shi ba.

Tawagar da aka yi garkuwa da itan dai ta hada da dakarun soji masu sa ido daga kasar Jamus, da wakilai daga kasar Denmark, Poland, Sweden da jamhuriyar Czech.