Jamiyyar APC ta yi zabe a Bauchi da Gombe

Image caption APC ta yi zaben shugabanni

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato APC ta gudanar da zabukan shugabanninta a wasu Jihohi da suka hada da Gombe da Bauchi.

Dama dai jam'iyyar wadda aka kafa ta a bara sakamakon hadewar wasu jam'iyyun adawa wuri guda, ba ta da zababbun shuwagabanni inda ta kasance hannun shuwagabannin riko.

Sai dai a Jihar Gombe inda akai yi zaben babu hamayya inda aka yi zaben e ko a'a.

Amma wasu 'yan Jami'yyar sun kauracewa zaben inda suke cewa ba a shirya adalci a cikinsa ba.

Haka ma dai a Jihar Bauchi an yi zaben ne yayinda ake cece-kuce kan umarni na wani kotu da ya jibanci zaben.

Karin bayani