An kwashe Musulmai 1200 daga Bangui

Dakarun Faransa da na Kungiyar Tarayyar Afrika dake aikin kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun ce sun raka Musulmai sama da 1200 daga birnin Bangui zuwa garuruwansu na haifuhuwa dake wasu sassan kasar.

Mutanen, wadanda suna cikin Musulmi kalilan din da suka rage a birnin na Bangui, sun tashi ne cikin manyan motoci 18.

Ficewar su keda wuya sai wasu su ka farma unguwar tasu, su ka yi wasoson abinda suka bari a baya. Sa'annan kuma su ka yi kaca-kaca da masallacinsu.

Wani Musulmi mazauni birnin, Alhaji Hadi Kabara Wananga, ya gaya wa BBC cewa mutanen Musulman ne su ka nemi a kwashe daga wurin saboda barazanar da ake wa rayukansu.

Amma ya ce kwashe Musulman ba shi ne zai kawo karshen rikicin da ya addabi kasar ba.

Karin bayani