CAR: An kashe mutane 20

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na cikin bala'i

Mutane kusan 20 sun mutu a wani hari da aka kai a wani asibiti a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a karshen mako.

Daga cikin wadanda aka kashen hadda wasu shugabannin al'umma da kuma ma'aikata uku na kungiyar agaji ta Medecins sans Frontieres.

An kashe mutanen ne a wani gari mai suna Nanga Boguila da ke arewa maso yammacin kasar a ranar Asabar.

Dakarun Faransa da na Afrika suna ci gaba da ayyukan tabbatar da tsaro don kawo karshen tashin hankali na addinni a kasar da aka shafe fiye da shekara guda ana yi.

A ranar Lahadi, aka kwashe Musulmai 1,200 a Bangui babban birnin kasar zuwa wasu yankunan da ke arewacin kasar.