Hukuncin kisa kan mutane 700 a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Masar ta haramta kungiyar 'yan uwa Musulmi

Wani Alkali a Masar ya yanke hukuncin kisa ga mutane kusan 700, na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ciki har da shugaban kungiyar Muhammed Badie.

An yanke wa mutanen hukuncin ne sakamakon rikicin da aka yi a birnin Minya a bara, inda mutane suka mutu sannan aka raunata 'yan sanda.

An mika shari'ar zuwa babban Mufti na Masar domin ya sake nazarin shari'ar, kafin zartar da hukunci a watan Yuni.

Kotun ita ce ta yanke hukuncin kisa a kan 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, kusan 40 a watan da ya gabata.

Sannan kuma ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan mutane kusan 500.

Karin bayani