Korea ta Kudu ta fara gwajin makamai

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kin Jong Un Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba wannan ne karo na farko da Korea ta Arewar ki atisaye irin wannan ba.

Ma'aikatar tsaron Korea ta Kudu ta ce Korea ta Arewa ta ta fara gwajin atisaye makamai a kusa da tekun da ke iyakar kasarta da Korea ta Kudu.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin wata guda da Korea ta Arewar ke yin atisaye irin wannan,wancan lokacin dai sai da kai da an yi musayar wuta da Korea ta kudu.

Korea ta Kudu ta ce an shaida mata wannan atisaye za a yi shi ne a kusa da tsubaran nan guda biyu da ake takaddama akansu da yammacin Korea.

A bangare daya kuma kakakin gwamnatin Korea ta Kudu yace dakaarun sojin kasar suna cikin shirin ko ta kwana.

ya kuma kara da cewa duk da cewa yankunan da aka ankarar da su na yakin Korea ta Arewar ne, sojojin Korea ta Kudu sun shirya tsaf domin kare fararen hula da kuma jiragen ruwa na fararen hula.

Korea ta Kudun ta kumashaidawa Korea ta Arewar cewa za su maida martani idan har ta shigo iyakarsu.