Microsoft ya kammala sayen Nokia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wayar Nokia ta kusa zama tarihi

Kamfanin kera manhajojin kwamfyuta Microsoft ya kammala sayen masana'antar Nokia mai sarrafa wayar salula a kan fam biliyan hudu da rabi.

Tun farkon wannan shekara, ya kamata a kammala wannan ciniki tsakanin kamfanonin biyu, sai dai tsaikon da aka samu wajen amincewar hukumomi masu kula da ayyukan kamfanonin ya kawo jinkiri.

Cinikin zai kawo karshen aikin kera wayoyin salula daga kamfanin Nokia.

Babban jami'in kamfanin Microsoft, Satya Nadella ya ce "A yau muna maraba da harkokin aikace-aikace da hajojin Nokia zuwa cikinmu."

"Kadarori da kere-keren wayar salula da za su zo da su, ba shakka za su inganta sauye-sauye a kamfaninmu," in ji Nadella.

'Makomar Nokia'

Kamfanin Nokia na kasar Finland a yanzu zai maida hankali wajen samar da hanyoyin sadarwar intanet da ayyukan tsara taswira da bunkasa fasaha da ba da lasisi-lasisi.

Masana'antun Nokia biyu ne wannan ciniki bai hada da su ba - da bangaren wata masana'antar kamfanin da ke Chennai, a India, har zuwa lokacin da hukumomin harajin kasar za su saki kadarorin masana'antar, sai kuma masana'antar Masan ta Koriya ta kudu, da ake shirin rufewa.

Da wannan ciniki, tsohon babban jami'in Nokia, Stephen Elop a yanzu ya zama mataimakin shugaban kamfanin Microsoft, mai kula da wayoyin salular Lumia na zamani da kwamfyutocin hannu sai kuma wayoyin salula na Nokia, da manhajar Xbox da ta Microsoft Surface.

Karin bayani