BBC ta shiga yankin Aleppo a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption BBC ta shiga yankin Aleppo a Syria

BBC ta samu wata dama da ba kasafai ake samu ba, ta shiga yankin da 'yan tawaye suke a Aleppo, birni mafi girma a Syria.

Birnin dai ya fuskanci hare-hare da dama ta sama, daga dakarun gwamnatin Syria.

Wakilin BBC ya ce watannin da aka shafe ana kai hare-hare ya yi matukar illa ga yankin, inda a yanzu gidaje da dama babu kowa a cikinsu saboda mutane sun tsere.

Rahotanni sun ce dubban mutane ne suka rasa rayukansu a watannin farko na wannan shekarar, wasu da dama kuma suka jikkata.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da kaddamar da haramtaccen yaki ta sama kan fararen hula.

Sai dai gwamnatin Syria na cewa tana kai hare-haren ne akan 'yan ta'adda.

Karin bayani