Za mu iya ceto 'yan matan Chibok —Matasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matasa sun ce a kara kaimi don ceto yan matan Chibok

Wani matashi dan banga a Jihar Borno da ake musu lakabi da Civilian JTF ya shaidawa BBC cewa matsawar aka sa kaimi sosai za a iya ceto 'yan matan nan 'yan makaranta da aka sace a Jihar.

Yanzu makonni biyu kenan tun bayan da aka sace dalibai 'yan mata a garin Chibok da ke jihar Bornon wadanda har yanzu ba a ga da yawa daga cikin su ba.

Sai dai wani matashi -- daya daga cikin samarin da ke taimakawa sojoji wajen tabbatar da tsaro wato Civilian JTF -- ya ce sun je dajin Sambisa ba sau daya ba ba sau biyu ba, wurin da ake kyautata zaton ana tsare da 'yan matan.

Matashin ya shaidawa BBC cewa, " 'yan matan basu bata ba; sai dai kawai ba tsawaita aiki bane idan aka tsawaita aiki ba zasu jima ba zasu fito insha Allahu amma akan iyakar Nigeria da Kamaru da Chadi suke kai kawo".

Koda yake yace 'yan bindigar da suka sace matan babu wani takamaiman wuri da suka ajiye su a cikin dajin.

A wata hira da yayi da BBC Shugaban kungiyar cigaban al'ummar Chibok, Dr Pogu Bitrus ya yi zargin cewar sun samu labarin an tsallaka da wasu daga cikin 'yan matan ta tafkin Chadi, Sai dai kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbarda wannan ikirarin.

Karin bayani