'Masu cutar sankara na iya tsawon rai'

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption An shigar da sabbin mutanen da ke dauke da cutar, cikin bayanan inganta kula da lafiyar masu Sankara

Alkaluma sun nuna cewa rabin mutanen da aka gano suna dauke da cutar sankara ko daji a Ingila da yankin Wales, za su iya rayuwa ta akalla shekaru 10, ninkin adadin baya a shekarun 1970.

Sabbin hanyoyin kula da masu cutar, sun bayar da gagarumar gudunmawa da kuma ganowa da kuma tantance cutar da wuri.

Sai dai Cibiyar bincike kan cutar Kansa ta Burtaniya, da ta yi wannan bincike ta ce ci gaban da aka samu, na nuna bukatar bullo da sabbin manufofin kai wa ga nasara.

Cibiyar ta ce tana son ganin masu cutar daji da ke rayuwa tsawon shekaru 10 sun karu zuwa kaso 75 cikin 100 nan da shekaru ashirin masu zuwa, domin haka ta ci alwashin kara rabin kudin da take kashewa cikin ayyukan bincike.

Hakkin mallakar hoto SPL

Masu bincike sun ce babu bukatar a rika ganin cutar kansa a matsayin wata "kibiyar ajali", kamar yadda yake a baya, amma sabbin alkaluma na nuna cewa an kai wani gaci.

Muhimmin Ci gaba

Kididdiga ta nuna cewa kaso 50 cikin 100 na mutanen da aka gano sun kamu da cutar kansa ne suka mutu a shekarun 1971 zuwa 1972.

Yanzu kuma kaso 50 ne ke yin tsawon rai zuwa akalla shekaru 10, sama da kaso 24 cikin 100 a 1971 zuwa 1972.

Sai dai wasu binciken da aka gudanar kan masu fama da cutar daji fiye da miliyan bakwai, sun kuma nuna cewa wasu masu cutukan Kansa har yanzu ba sa tsawon rai sosai.

Ga misali, kaso biyar cikin 100 ne kadai na masu fama da Sankarar huhu ake sa ran za su yi tsawon rai zuwa shekaru 10.

Babban jami'in Cibiyar binciken Kansa na Burtaniya, Dr. Harpal Kumar ya ce "Ban taba sa ran samun ci gaban da aka cimma yanzu ba. A hankali dai muna dakile wannan mummunar cuta. Ko da yake har yanzu cutar na ajalin wasu mutane, ba shakka sai mun magance haka"

Cibiyar ta zayyana wasu muhimman fannoni da za a maida hankali a kansu, domin ci gaban da aka samu ya dore.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Fannonin sun hadar da zuba kudi cikin ayyukan yi wa masu cutar magani, rage shan taba sigari da mayar da hankali a kan cutukan daji da ke saurin hallaka masu fama da su.