Jonathan ya cire Ahmed Gulak

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ahmed Ali Gulak

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya cire mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Barrister Ahmed Ali Gulak nan take.

Kakakin Shugaban kasar, Mr Reuben Abati wanda ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter, ya ce Shugaba Jonathan ya gode wa Mr Gulak saboda gudunmuwar da ya bayar a cikin gwamnatinsa.

A cewar Abati, nan gaba za a nada wanda zai maye gurbin Barrister Gulak din.

Sanarwar ta Mr Abati ba ta yi karin haske ba kan abin da ya sa aka cire shi, amma masu sharhin siyasa na kallon matakin a matsayin abin mamaki, ganin yadda Gulak ke kare gwamnatin Jonathan kai da fata.

Karin bayani