Malala ta bukaci a saki 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Malala ta ce wajibi ne gwamnatin Nigeria ta ceto 'yan makarantar Chibok

Yarinyar nan 'yar Pakistan da Taliban suka harba a ka a shekarar 2012, Malala Yousafzai ta yi kira ga gwamnatin Nigeria ta dauki dukkan matakai na ceto 'yan matan Chibok.

Malala ta shaidawa BBC cewa ya kamata gwamnati ta sani tana da ''babban nauyi'' a kanta na tabbatar an saki 'yan matan.

A cewarta, ta yi matukar kaduwa da jin labarin sace 'yan makarantar, tana mai cewa ya kamata dukkanin kasashen duniya su hada hannu wajen ganin an ceto yaran.

Malala ta ce bai wa 'ya'ya mata ilimi wajibi ne, kuma hakkin kula da su na kan gwamnatin kowacce kasa.

Ta ce musulinci ya wajabta a bai wa mata ilimi, domin haka duk mutumin da ke yin tarnaki a kan hakan ba musulmi na gari ba ne.

Karin bayani