Kasuwar wayar Samsung ta ragu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Samsung ya ce ribar da yake samu daga wayoyin hannu ta karu da kashi 18

Kamfanin Samsung ya bayyana cewa yawan cinikin da yake ya ragu da kashi hudu cikin dari.

Kudin shigar kamfanin a wannan bangare ya ragu zuwa dala tiriliyan 33.4 daga watan Janairu zuwa Maris.

Sai dai kamfani na Koriya ta Kudu ya ce ribar da yake samu daga wayoyin hannu ta karu da kaso 18 cikin 100 a watanni uku da suka gabata.

Samsung dai shi ne kamfani kera wayar hannu mafi girma a duniya kuma wayar ce ke samarwa kamfanin da kaso mafi yawa a ribar da yake samu.

Samun wannan kididdiga ya biyo bayan alkalaman da shahararren kamfanin ya fitar inda ya ce ya sami riba da yawan ta yakai tiriliyan 7.57 a watanni uku na farkon bana ba kamar sauran watanni uku da suka gabata ba inda ya sami tiriliyan 7.3.

'Bunkasar kasuwa'

Wayoyin komai- da- ruwanka na Galaxy da kamfani Samsung ke samarwa sun taimaka wajen bunkasar kamfani.

Sun kuma taimaka wajen dakile kasuwar kamfani Nokia wanda shi ne kamfani mafi girman da ke kera wayoyin hannu a duniya cikin shekarar 2012.

Haka nan, gasa sai karuwa take wadda ke tilastawa kamfanoni rage farashin kayyayakin su.

A dalilin haka ne ma kasuwar wayar komai da ruwanka ke kara yin kasa.

Karin bayani