'Yan matan Chibok hudu sun tsere - Moro

Image caption Sace 'yan mata kusan 200 ya ja hankalin kasashen duniya

Ministan cikin gidan Nigeria ya ce an gano wasu karin 'yan matan Chibok hudu, da suka tsere daga hannun 'yan bindigar da suka sace su.

Patrick Abba Moro ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce an gano daliban a garin Monguno dake jihar Borno a arewacin kasar.

Haka kuma ya kara jaddada kokarin da gwamnati ke yi, wajen ganin an ceto 'yan matan da aka sace sama da makonni biyu.

Iyaye da 'yan uwan 'yan matan dai sun nuna rashin jin dadi, game da rashin samun cikakken bayani kan abin da gwamnati ke yi kan batun.