Ana gudanar da zabe a Iraqi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zabe a Iraqi

Masu kada kuri a sun tafi rumfunan zabe a Iraqi a zaben 'yan majalisu na farko a kasar tun bayan da Sojin Amurka suka janye daga Iraqi a 2011.

Firai Ministan kasar mai ci Nouri al-Maliki yana neman wa'adi na uku a karagar mulki amma Kamfe din na fuskantar turjiya bisa karin tashe-tashen hankulan siyasa.

Wakilin BBC ya ce jiragen soja masu saukar ungulu na ta shawagi a sararin samaniyar Baghdaza, gwamnati kuma ta rufe filin tashin jiragen sama da manyan hanyoyin shiga da fitar birnin na wucin gadi.

Ba za a kada kuri'a a wasu yankunan da 'yan Sunni suke ba da ke yankin Anbar, inda gwamnatin hadaka ta Mr Maliki wadda 'yan shi'a ke jagoranta ke ta kokarin dakile tada kayar baya a Falluja, da wata Kungiya dake da alaka da Alqaeda ke jagoranta.

Karin bayani