Gidajen ma'aikata za su lashe $6bn a Nigeria

Image caption Akasarin ma'aikatan Najeriya suna zama a gidajen haya

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan zai aza harsashin aikin gina gidajen Ma'aikatan kasar, wanda zai lashe dala biliyan shida.

Aikin wani hadin gwiwa ne tsakanin babbar kungiyar kwadago ta kasar NLC, da wani kamfanin gine-gine mai zaman kansa, inda a karkashinsa za a gina gidaje a dukkan jihohi 36 na Nijeriya.

Kididdigar Bankin duniya dai ta nuna cewa gidaje miliyan 17 ake bukata domin cike gibin gidaje ga mutanen kasar.

Sai dai fatan al'ummar kasar shi ne wadanda aka yi abin domin su, su amfana.