Chibok: Daruruwan mata sun yi gangami

Image caption Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Abuja bai hana matan gangamin ba

Daruruwan mata da suka halarci gangamin da aka yi a Abuja da ke Nigeria, sun mika wasikar koke na neman gwamnati ta kara kaimi wajen ceton 'yan matan Chibok.

Matan sun yi jerin gwano dauke da kwalaye kuma sun samu rakiyar jami'an tsaro zuwa majalisar dokokin kasar, inda suka mika takardar ga shugaban majalisar, Sanata David Mark.

Shugaban majalisar ya maida martani da cewa suma iyaye ne, saboda haka hankalinsu a tashe yake.

Ya kuma bai wa matan tabbacin cewa daga yanzu za a dinga bayyana halin da ake ciki, game da ceton 'yan matan daga lokaci zuwa lokaci.

Sama da makonni biyu kenan da aka sace 'yan matan, kuma kawo yanzu ba a san inda kusan 200 suke ba.

Ana dai zargin kungiyar Boko Haram da sace 'yan matan a makarantar sakandare da ke Chibok a jihar Borno.