Za a yi zagaye na bakwai a zaben India

Narendra Modi dan takara a India Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za dai a tafi zagaye na bakwai na zaben da ake gudanarwa a India.

Za a tafi zagaye na bakwai a zaben da ake gudanarwa a kasar India, wanda kusan mutane miliyan dari da arba'in suka kada kuri'unsu a jihohi tara ciki har da Andhra Pradesh.

Da zarar an kammala zagaye na karshe na zaben a ranar sha biyu ga watan mayu, fiye da mutane miliyan dari takwas ne suka kada kuri'ar a zabe mafi girma a duniya.

Gwamnati mai mulki ta jam'iyyar Congress na fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar adawa ta Hindu Nationalist BJP.

Narendra Modi dan jam'iyyar ta BJP da a yanzu ya ke da matukar farin jini watakil ya zama Prime Ministan kasar, kuma a yau zai kada kuri'a a jiharsa wato Gujarat.

Mr Modi dai wani mutum ne mai wuyar sha'ani, a lokacin shugabancin sa jihar Gujarat ta fuskanci zanga-zangar musulmai mafi muni a shekarar 2002.

Za a kuma akirga kuri'un zaben a ranar sha shida ga watan Mayun wannan shekarar.