'Dalibai 'yan mata 276 aka sace a Chibok'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Iyayen 'yan matan na cikin zullumi

Rundanar 'yan sanda a jihar Borno da ke Nigeria ta ce adadin 'yan matan da aka sace a makarantar sakandare ta Chibok ya kai 276.

Wannan adadin ya zarta yawan da aka kiyasta tun farko da karin 'yan mata 30 bisa alkaluman da aka fitar bayan sace 'yan matan a ranar 14 ga watan Afrilu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Lawal Tanko ya shaidawa BBC cewar sun samu wannan adadin ne sakamakon bayanan da suka samu daga wajen shugabar makarantar 'yan matan da ke Chibok.

Lawal Tanko ya ce "Daga jawabin da muka samu daga Principal, za su kai yara kusan 276 da aka sace, sannan akwai kusan 53 da suka kubuta".

A cewarsa a yanzu adadin 'yan matan da ake nema ya kai 223.

Ya kara da cewar "Muna rokon iyaye su bamu hotunan 'ya'yansu domin tabbatar da wannan adadin, saboda ita makaranta duka takardunta sun kone".

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewar akwai daliban makarantu da dama da aka kai su Chibok domin rubuta jarabawa bayan da aka rufe sauran makarantun sakandare a jihar ta Borno.

Masu sharhi na cewar a yanzu haka Nigeria na tsaka mai yuwa saboda baya ga sace 'yan matan, an kuma kai hare-hare sau biyu a Abuja, babban birnin kasar inda mutane kusan 94 suka mutu sannan wasu kusan 200 suka samu raunuka.

Karin bayani